A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Hujjatul Islam wal Muslimin Sayyid Ja’afar Alawi, shugaban Gidan Talabijin din Wilayat na Duniya, a yayin ganawarsa da Hujjatul Islam wal Muslimin Tusi, Darakta Janar na gidajen Rediyo da Talabijin (IRIB) Cibiyar Qom, ya bayyana cewa wannan zaɓi ya dace kuma ya yi daidai da damar kafofin watsa labarai da al’adun birnin Qom mai tsarki. Ya ce: "Qom a matsayin tushen yaɗa ma’arifar Ahlulbaiti (AS), kuma da albarkar Kareematu Ahlulbaiti (AS) (Sayyida Ma'asuma) da kuma Hauzozin ilimi, tana da matsayi na musamman wajen yaɗa koyarwar addini, kuma kafofin watsa labarai na addini za su iya amfani da wannan babbar dama wajen isar da ilimin Musulunci zuwa duk faɗin duniya."
Ya kuma yi nuni da tarihin aiki da kwarewar Darakta Janar na tashar Noor a fannin kafofin watsa labarai, inda ya ƙara da cewa: "cikakken sanin da Hujjatul Islam wal Muslimin Tusi yake da shi game da yanayin kafofin watsa labarai da kuma tsarin Gidan Talabijin na Wilayat, zai bude ƙofa ga mu’amala mai tasiri da haɗin gwiwa mafi faɗi.
Shugaban Gidan Talabijin din Wilayat na Duniya ya yi bayani kan damar ilimi da na abun ciki da tashar ke da su, yana mai cewa: "Tashar Wilayat a cikin shekaru da suka gabata ta hanyar amfani da fitattun malamai na Hauza da ƙungiyoyin ilimi na musamman, ta iya samar da shirye‑shiryen ilimi tare da sa ido da kulawar manyan malamai, ulama da masana; damar da kafofin watsa labarai na ƙasa ma za su iya amfani da ita wajen samarwa da watsa shirye‑shiryen addini da aƙida.
Haka kuma ya bayyana shirye‑shiryen Wilayat na yin haɗin gwiwa wajen watsa wasu shirye‑shiryen ilimi a lokaci guda, da samar da abubuwan haɗin gwiwa, da kuma amfani da juna wajen kayan aiki na watsa labarai. Ya ce: "shirye‑shirye da dama na musamman a fannonin hukunce-hukunce (ahkam), aƙida, amsa ga shubuhohi, shirye‑shiryen Alƙur’ani, tarihi, addinai da mazhabobi, da salon rayuwa tare da fitattun malaman Hauza ana samar da su a Wilayat; kuma za a iya ba da su ga kafofin watsa labarai na ƙasa da kuma tashar Noor a cikin tsarin haɗin gwiwa."
Hujjatul Islam wal Muslimin Alawi ya kuma yi nuni da ayyukan Wilayat na harsuna da dama, yana mai cewa: Wilayat ta harshen Farisanci ana iya kallonta ta hanyar Telewebion ma.
A ɓangaren nasa, Hujjatul Islam wal Muslimin Tusi, Darakta Janar na IRIB Cibiyar Qom, ya gode wa ayyukan Gidan Talabijin din Wilayat n'a Duniya, ya taya Hujjatul Islam wal Muslimin Alawi murnar sake naɗa shi a matsayin shugaban Wilayat, tare da jaddada buƙatar faɗaɗa haɗin gwiwar kafofin watsa labarai. Ya ce: "Wilayat na da wata damar da ba kasafai ake samu ba ta fuskar masana addini da ma’arifa, kuma wannan dama na iya taimakawa sosai wajen samar da shirye‑shiryen haɗin gwiwa."
Ya ƙara da cewa: samar da shirye‑shiryen haɗin gwiwa—musamman a fannin shirye‑shiryen kai tsaye, aƙida da ahkam—na iya ƙara haɓaka haɗin kai da ƙarfafa juna tsakanin kafofin watsa labarai na ƙasa da tashar Wilayat."
Darakta Janar na IRIB Cibiyar Qom ya kuma yi nuni da nasarorin da aka samu a baya wajen samar da shirye‑shiryen haɗin gwiwa da wasu tashoshin waje, yana mai cewa: "Akwai yiwuwar haɗin gwiwa a shirye‑shiryen Hausa (Afirka), Larabci, da Azeri ma, kuma ta hanyar amfani da damar masana da fassarar kai tsaye, za a iya gabatar da ingantattun abubuwan watsa labarai ga masu sauraro na duniya.
A ƙarshe, ɓangarorin biyu sun jaddada ci gaba da mu’amala da tsara shirye‑shirye don faɗaɗa haɗin gwiwar kafofin watsa labarai domin yaɗa ma’arifar Ahlulbaiti (AS).
Ra'ayinka